Wata babbar kotu a jihar Oyo ta umarci jam’iyyar PDP tare da mukaddashin shugabanta na kasa, Umar Damagum, da su ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron kasa na jam’iyyar da aka tsara ranar 15 ga Nuwamba a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Mai shari’a A.L. Akintola ne ya bayar da wannan umarni a ranar Litinin yayin da yake yanke hukunci kan wata bukatar gaggawa da Folahan Malomo Adelabi ya shigar.
Hukuncin kotun ya zo ne a daidai lokacin da ake samun rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar PDP kan tsarin shugabanci da kuma shirye-shiryen taron da ake sa ran zai tantance muhimman mukamai da dabarun jam’iyyar kafin zaben 2027.
