Trend News Hausa
Labarai

‘Yan Najeriya sun yi sa’a Tinubu na jure suka – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce ’yan Najeriya sun yi sa’ar samun shugaba irin Bola Ahmed Tinubu da yake jure suka ba tare da daukar mataki ba.

Wike ya yi wannan magana ne a Abuja yayin kaddamar da titin Arterial Road N1 a Wuye, inda ya yi nuni da rubutun Omoyele Sowore da ya kira Tinubu “ɓarawo” a shafukan sada zumunta.

Ya ce ko a Amurka, babu wanda zai fito ya kira shugaban ƙasa “ɓarawo” kai tsaye.

Ministan ya kuma karyata jita-jitar cewa ya samu bugun zuciya, inda ya ce masu yada jita-jitar su ne za su ci gaba da samun bugun zuciya.

A kan yajin aikin likitoci a Abuja, Wike ya ce an ware naira biliyan 25 a kasafin 2025 domin ayyukan lafiya, yana mai jaddada cewa dole ne duk wani aiki ya bi ka’ida kafin biyan alawus ko daukar ma’aikata.

Ya kuma gargadi ma’aikatan Abuja da kada su yi amfani da aikin gwamnati wajen wasa da siyasa.

Related posts

Manufofin Tattalin Arzikin gwamantin Tinubu na Talauta ’Yan Najeriya – ACF

Editor In-Chief

Za mu tura sojoji ƙasar Ukraine idan bukatar hakan ta taso – Burtaniya

Ali Hamisu

Kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya a Jigawa

Editor In-Chief

Leave a Comment