Trend News Hausa
Siyasa

Da na so wa’adi na uku, na san yadda zan bi wajen cimma burina – Obasanjo

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi watsi da ikirarin cewa ya taɓa neman wa’adi na uku a ofis, inda ya jaddada cewa ba shi da wannan buri a lokacin mulkinsa.

A yayin jawabi a ranar Laraba, a taron tattaunawar dimokuraɗiyya da Gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a birnin Accra, Obasanjo ya ce babu wani ɗan Najeriya – mai rai ko wanda ya rasu – da zai iya tabbatar da cewa ya taɓa faɗa masa yana neman wa’adi na uku.

“Ina da hankali. Da na so wa’adi na uku, na san hanyar da zan bi wajen samunsa. Kuma babu wani ɗan Najeriya, mai rai ko mamaci, da zai ce na kira shi na faɗa masa ina son wa’adi na uku,” in ji Obasanjo.

Ya kuma jaddada cewa ya riga ya cimma manyan abubuwa masu wahala, inda ya kawo misali da samun rangwamen bashi ga Najeriya a lokacin mulkinsa, wanda ya ce ya fi wahalar samu fiye da wa’adi na uku.

“Ina ta gaya musu cewa, ku duba, da na so samun rangwamen bashi wanda ya fi wahalar samu fiye da wa’adi na uku, na samu shi. To da na so wa’adi na uku, da na samu shi ma,” in ji shi.

Related posts

Tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark ya fice daga jam’iyyar PDP

Ali Hamisu

Ina nan zama daram a PDP, in ji Gwamna Adeleke

Ali Hamisu

Dalilan da yasa PDP ta mika tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa ga Kudu – Bala Mohammed

Ali Hamisu

Leave a Comment