Trend News Hausa
Labarai

Ganduje ya yi ta’aziyya ga Shugaban NNPCL Mele Kyari bisa rasuwar ɗiyarsa

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana babban alhini da ta’aziyya ga Shugaban Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL), Mallam Mele Kyari, bisa rasuwar ɗiyarsa , Fatima Kyari.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na shugaban jam’iyyar, Edwin Olofu, ya sanya wa hannu, Dr Ganduje ya bayyana rasuwar ‘yar Mallam Kyari a matsayin babban rashi, ba kawai ga iyali ba har ma ga duk wanda ya santa da ƙaunar ta.

Ya bayyana jimamin da ahalin jam’iyyar APC ke ciki tare da cewa babu kalmomi da za su iya bayyana cikakkiyar zafin rasa ɗa.

“Tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da Mallam Mele Kyari da dukan iyalinsa a wannan mawuyacin lokaci. Muna addu’a Allah (SWT) ya ba wa mamaciyar hutun ta har abada, kuma ya ba wa iyalin ƙarfin zuciya don jure wannan babban rashi,” in ji Dr Ganduje.

Ya kuma yi addu’ar samun rahamar Allah ga iyalin da suka yi rashin, tare da ƙarfafa su da su yi haƙuri da sanin cewa wa’adin diyarsu a duniya ya ƙare.

Related posts

An kama matar da ta jefar da jaririnta a gefen hanya

Editor In-Chief

Boko Haram ta kashe sojoji da fararen hula a Borno

Editor In-Chief

Badakalar N17bn: Kamfanonin jiragen yawo za su maka NAHCON a kotu

Editor In-Chief

Leave a Comment