Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da kuma masu ɗaukar nauyin ayyukan rashin tsaro, inda ya ce dole ne su mika wuya ko kuma su fuskanci hallaka.
Tinubu ya bayyana cewa gwamnati ba za ta nuna wani jinkai ga waɗanda ke zubar da jinin ’yan Najeriya ba.
A cikin jawabin da ya gabatar kai tsaye ta talabijin domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta shekarar 2026 a ranar Juma’a, shugaban ƙasar ya ce damar da gwamnati ta bayar na karɓar tuban masu tayar da kayar baya ba za ta kasance a buɗe har abada ba.
Da yake magana kan sace yara da malamansu da aka yi kwanan nan a jihohin Oyo da Borno, Tinubu ya ce har yanzu gwamnati na da fata cewa za a ceto su kuma su dawo gida lafiya.
Ya ce wannan ne ya sa gwamnatinsa ta ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro tare da amincewa da ɗaukar sama da sabbin jami’an ’yan sanda 50,000 da kuma dubban sojoji domin ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro.
“Kasafin kuɗin shekarar 2026 ya ware naira tiriliyan 5.41 domin tsaro da kariya, wanda shi ne mafi girma a tarihin ƙasar. Gwamnatinmu a shirye take ta yi fiye da haka domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a,” in ji Tinubu.
Ya ƙara da cewa Najeriya ta sauya daga horo tare da ƙawayenta kamar ƙasar United States, France da wasu ƙasashen Turai zuwa kai hare-haren da aka tsara daidai kan maboyar ’yan ta’adda.
Tinubu ya ce a yankin Arege da ke jihar Borno State, jami’an tsaro sun lalata cibiyar jagorancin ƙungiyar ISWAP, yana mai cewa adadin mutanen da ta’addanci ke kashewa ya ragu da kashi 81 cikin ɗari tun daga shekarar 2015.
A cewarsa, sama da ’yan ta’adda 13,000 aka kashe a cikin shekara guda da ta gabata, yayin da sama da mayaƙa 124,000 da iyalansu suka ajiye makamansu tun daga shekarar 2023 ta hanyar shirin Operation Safe Corridor.
Shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai tare da gujewa ɗora laifin ayyukan ta’addanci a kan wata ƙabila ko al’umma.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa Najeriya za ta yi nasara a yaƙin da take yi da ta’addanci tare da ci gaba da gina ƙasa mai wadata da zaman lafiya.
Tinubu ya yabawa jami’an tsaro, ciki har da sojoji, ’yan sanda da hukumomin leƙen asiri saboda sadaukarwar da suke yi wajen kare ƙasar.
“Najeriya na gaishe ku saboda sadaukarwar da kuke yi,” in ji shi.
Haka kuma ya gode wa sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da na al’umma bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da sulhu, yana mai cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya magance matsalolin tsaro ba tare da haɗin kan jama’a ba.
