Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) ta bayyana cewa halin lafiyar Nnamdi Kanu ba mai hatsarin ba ne.
A hukuncin da aka yanke ranar 26 ga Satumba, Mai Shari’a James Omotosho, wanda ke jagorantar zaman kotun, ya bayar da umarni ga shugaban NMA da ya kafa kwamitin bincike domin tantance matsayin lafiyar wanda ake tuhuma.
Omotosho ya bayar da wannan umarni ne yayin da yake yanke hukunci kan wata ƙara da ke neman a mayar da Kanu, shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, daga hannun hukumar DSS zuwa Asibitin Ƙasa da ke Abuja domin jinya.
Shugaban IPOB ɗin ya yi ikirarin cewa lafiyarsa ta tabarbare tun bayan tsare shi, yana mai nuna rahotannin likitoci da ke cewa yana fama da matsalolin hanta da ƙoda da ciwon kumburi.
Sai dai masu gabatar da ƙara sun soki wannan buƙata, suna mai jaddada cewa gwamnatin tarayya ta samar masa da cikakkiyar kulawar lafiya a inda yake tsare.
A zaman kotu da aka gudanar ranar Alhamis, Lauyan masu gabatar da ƙara, Adegboyega Awomolo, ya bayyana cewa rahoton NMA an karɓe shi kuma an mika shi kotu tun ranar 13 ga Oktoba, kuma an raba wa lauyoyin biyu.
Lauyan wanda ake tuhuma, Kanu Agabi, ya tabbatar da cewa sun karɓi rahoton.
A cikin rahoton da aka karanta a bainar jama’a, kwamitin NMA ya kammala da cewa Kanu yana da ƙoshin lafiya don fuskantar shari’a.
