Trend News Hausa
Siyasa

Amaechi ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwani na ADC

Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, yana mai zargin cewa an tafka magudi da hana mambobi da dama kaɗa ƙuri’a.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Amaechi ya bayyana sakamakon zaɓen a matsayin wanda aka shirya tun farko, yana cewa ba za a amince da shi ba sai idan an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.

Ya ce kusan kashi 80 cikin 100 na mambobin jam’iyyar ba a ba su damar kaɗa ƙuri’a ba, yana tambayar abin da zai bambanta ADC da sauran jam’iyyu idan aka yi irin wannan zargin magudi.

Related posts

Kwamitin amintattu na PDP na gudanar da taron gaggawa

Ali Hamisu

‘Da sa hannunka wajen ƙaruwar talauci a Najeriya’ — Sanwo-Olu ya kalubalanci Obi kan maganganunsa a jami’a a Amurka

Ali Hamisu

Ana zargin Mataimakin Gwamna’ya mari’ Minista a gaban Mataimakin Shugaban ƙasa a Bauchi

Ali Hamisu

Leave a Comment