Trend News Hausa
Siyasa

Ƴansanda sun rufe hanyoyin zuwa wajen taron amincewa da Jonathan a matsayin dan takarar PDP

Jami’an ‘yansanda sun kulle hanyoyin da ke kaiwa cibiyar taron musamman da wani bangare na jam’iyyar PDP ke shirin gudanarwa domin amincewa da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027.

Bangaren PDP karkashin jagorancin Kabiru Turaki ya shirya gudanar da taron ne a Abuja, duk da adawar bangaren da ministan Abuja, Nyesom Wike, ke marawa baya. Matakin ya biyo bayan umarnin Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) da ta bukaci cibiyoyin taruka su yi hulda ne kawai da shugabannin jam’iyyun da INEC ta amince da su.

Sakataren yada labarai na bangaren Turaki, Ini Ememobong, ya ce sun cika dukkan sharuddan gudanar da taron kuma za su ci gaba da shirinsu kamar yadda aka tsara. Sai dai rahotanni sun nuna cewa an sauya wurin taron zuwa wani wuri a Area 10 da ke Abuja bayan kulle hanyoyin zuwa wurin da aka fara warewa.

Related posts

Babu wani ɗan Najeriya mai kishin ƙasa da zai goyi bayan Tinubu a 2027 – PDP

Ali Hamisu

Idan har Tinubu bai lashe zaɓen shugaban ƙasa a Edo ba, zan yi murabus – Gwamna Okpebholo

Ali Hamisu

Da Ɗumi-Ɗumi: KANSIEC ta rage kuɗin fom ga ƴan takara a zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Ali Hamisu

Leave a Comment