Trend News Hausa
Labarai

Na sha wahala da kalubale kafin na zama shugaban ƙasa – Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ya fuskanci matsin lamba na siyasa, ƙalubalen shari’a da kuma wahalhalu masu yawa kafin ya samu nasarar zama shugaban Najeriya.

Tinubu ya yi wannan bayani ne a ranar Juma’a yayin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar gwamnonin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a gidansa da ke Lagos. Ya ce ya yi tafiyar neman shugabancin ƙasa cikin yanayi mai cike da ƙalubale, amma bai yi kasa a gwiwa ba duk da matsalolin da ya fuskanta.

Shugaban ƙasar ya ce ya ci gaba da bin manufofinsa na yaƙin neman zaɓe ba tare da bayyana dukkan dabarunsa ba, yana mai yabawa gwamnoni da suka mara masa baya duk da haɗarin siyasa da suka ɗauka. Ya ce gwamnatinsa ta tsallake ƙalubalen shari’a da zarge-zarge daban-daban, tare da kare ƙasar daga durƙushewar tattalin arziki.

Tinubu ya kuma gode wa gwamnoni bisa goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa da kuma yadda suke ƙarfafa amincewar jama’a ga gwamnati duk da sauye-sauyen tattalin arziki da aka aiwatar. Ya ce tattalin arzikin ƙasar ya samu ci gaba, noma yana bunƙasa, yayin da jihohi ba sa dogaro da tallafin gaggawa daga gwamnatin tarayya domin biyan albashi kamar yadda ake yi a baya.

Shugaban ƙasar ya yi waɗannan kalamai ne a daidai lokacin da yake bikin cika shekaru uku a mulki bayan an rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023, inda ya gaji Muhammadu Buhari. Ya kuma yaba wa ’yan Najeriya saboda haƙuri da juriya da suka nuna wajen fuskantar ƙalubalen da suka biyo bayan gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatinsa.

Related posts

Jiragen yaƙin sojin Najeriya sun lalata mafakar ƴan bindiga a Katsina

Editor In-Chief

‘Yan bindiga sun kashe shugaban rikon kwarya na Miyetti Allah a jihar Katsina

Ali Hamisu

Kaduna: Yadda Sojoji suka harbe ‘yan fashin daji da suka zo daukar kudin fansa

Ali Hamisu

Leave a Comment