Trend News Hausa
Labarai

Hukumar tace fiina-finai ta Kano ta jagoranci wasu mata uku masu sana’ar Gala zuwa karɓar addinin Musulunci

Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta jagoranci wasu mata uku masu sana’ar wasan Gala zuwa ga karɓar addinin Musulunci bayan sun nuna ra’ayinsu na rungumar addinin da kansu.

A wata sanarwa da Hukumar ta fitar ranar 19 ga watan Mayun 2026, ta ce an gudanar da taron ne cikin wani biki na farin ciki da aka shirya a harabar dakin taron Hukumar, inda shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha, ya jagoranci matan wajen karɓar addinin Musulunci.

Shugaban Hukumar ya bayyana ranar a matsayin daya daga cikin ranakun da suka fi ba shi farin ciki a rayuwarsa, yana mai cewa shawarar da matan suka yanke ta samo asali ne daga kyawawan halaye, zaman lafiya da kuma mu’amala ta gari da suka gani daga abokansu Musulmi a masana’antar nishadi.

Sanarwar ta ce matan ukun da suka karɓi Musuluncin sun hada da Dicson da Zara daga Jihar Adamawa, sai Hannatu daga Jihar Gombe, wadanda suka dade suna gudanar da sana’ar Gala a Kano.

Matan sun bayyana jin dadinsu kan matakin da suka dauka, tare da godewa irin kauna da kyakkyawar mu’amala da suka samu daga abokansu da sauran jama’a a Kano.

Da take jawabi a madadin wadanda suka karɓi Musulunci, Hannatu ta ce kyawawan koyarwar addinin Musulunci da yadda Musulmai ke rayuwa cikin zaman lafiya da kyautatawa juna ne suka yi tasiri wajen yanke shawarar rungumar addinin.

Sanarwar ta samu sa hannun Abdullahi Sani Sulaiman a madadin shugaban Hukumar.

Related posts

Jaridar Leadership Ta Karrama Gwamnan Jigawa

Editor In-Chief

Kotu a Kano ta daure Kocin Ƙwallon kafa saboda Luwadi da Ƙaramin Ɗan Wasa

Ali Hamisu

Anambra: Mutum ɗaya ya mutu, shidda sun jikkata bayan kwamitin kar ta kwana ya yi harbi a kasuwar Onitsha

Ali Hamisu

Leave a Comment